Fargaba Ya Ƙaru Yayin da ’Yan Sanda Ke Ci Gaba da Tsare Tsohon Sarkin Kano Duk da Matsalolin Tsaro a Tsanyawa, Rimin Gado da Shanono

Duk da matsanancin rashin tsaro da ya addabi kananan hukumomin Tsanyawa, Rimin Gado da Shanono, jami’an rundunar ’yan sandan Kano da ke aiki a yankunan sun ci gaba da tsare tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a gidansa da ke Nassarawa.
Al’umman yankunan na ci gaba da fuskantar hare-hare daga ’yan ta’adda masu kai farmaki gida-gida, lamarin da ya sanya jama’a cikin ƙarin fargaba, musamman ganin yadda jami’an ’yan sanda ke mayar da hankali kan kare mutum ɗaya, maimakon dubban fararen hula da ke bukatar kariya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa har zuwa yanzu da wannan rahoto ke fitowa, rundunar ’yan sandan Kano ba ta janye jami’an da ta tura gadin tsohon Sarkin ba, duk da umarnin shugaban kasa da kuma na babban Sifeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya bukaci a janye duk wani jami’i da ke kula da wanda ba shi da mukamin da doka ta amince masa.
Wannan yanayi ya kara tayar da ce-ce-ku-ce a cikin jama’a, wadanda ke ganin fifita tsaron mutum ɗaya ya mayar da rayukan mutane fiye da 100,000 cikin hadari, musamman ma a lokacin da hare-hare ke kara yawaita a yankin.
A halin yanzu ana jiran ganin ko rundunar ’yan sandan Kano za ta bi umarnin da aka bayar ko kuwa za ta ci gaba da barin al’umma cikin tada-kai-da-waje bisa fifita wani da doka ba ta bai wa mukami ba.




