Kwalejin Tsaro ta Ƙasa (NDC) Ta Kammala Bincike a Jihar Kebbi Kan Harkar Noma

Wata tawaga daga National Defence College (NDC) Course 34, karkashin jagorancin Commodore AA Abu, ta kammala ziyarar kwana biyar a Jihar Kebbi domin nazarin damar noma da masana’antar sarrafa amfanin gona a matsayin dabarar ƙarfafa cigaban ƙasa da tsaro.
Commodore Abu ya bayyana haka bayan ziyarar girmamawa da suka kai wa Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, a fadar sa da ke Birnin Kebbi. Ya ce manufar ziyarar ita ce binciken yadda noma da sarrafa amfanin gona za su taka rawa wajen ƙarfafa tsaro da ci gaban Najeriya.
Ya jinjinawa Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, bisa matakan da ya ɗauka wajen bunkasa bangaren noma, musamman shinkafa, albasa da sauran kayan gona da ake iya fitarwa kasashen waje.
Tawagar, wacce ta haɗa da wakilai daga Tanzania da Benin, ta ziyarci gonaki, masana’antar nika shinkafa, ƙungiyoyin manoma da makarantu domin ganin yanayin aikin noma kai tsaye.
Kakakin Ma’aikatar Noma ta jihar, Hon. Shehu Muazu, ya ce sun nuna wa tawagar dukkan matakan harkar noma daga tushe zuwa matakin ilimi, inda suka sadu da manoma kuma suka gamsu da abin da suka gani.
Sarkin Gwandu ya yaba da wannan ziyara, yana mai cewa tana nuna kyakkyawar haɗin kai, tare da kira ga mahalarta su mayar da sakamakon bincikensu zuwa ayyukan da za su inganta tsaro, zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin ƙasa.




