Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya koma jam’iyyar APC, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a 2027

Kano, Najeriya —
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, tare da bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake neman wa’adin mulki a shekarar 2027.
Kofa ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce ya samu maraba daga dubban magoya bayansa a garinsu Kofa, cikin ƙaramar hukumar Bebeji, waɗanda suka yanke shawarar barin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya don shiga APC.
A cewarsa, sama da malamai 2,000 sun gudanar da addu’o’i na musamman domin Shugaba Tinubu da zaman lafiya da ci gaban ƙasar.
Ficewar Kofa daga NNPP na zuwa ne bayan rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar, musamman a Kano, tsakanin manyan shugabanni kan tsarin jagoranci da tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kofa, wanda tsohon Daraktan Tinubu Support Group ne, ya taba kasancewa a APC kafin komawarsa NNPP a 2022, amma yanzu ya dawo jam’iyyar mai mulki, abin da ke nuna sabuwar matsaya a siyasar Kano.




