Siyasa

Shugaban APC na Kano ya ja kunnen ‘ya’yan jam’iyya kan cece-kuce game da nadin shugaban NERC

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji duk wani abu da zai janyo rabuwar kai ko tashin hankali a cikin jam’iyyar, musamman kan batun tabbatar da nadin Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Lantarki ta Kasa (NERC).

A wata sanarwa da aka aikawa ahrasjo news Abbas ya nuna damuwa kan yadda cece-kuce kan wannan batu ke kara raba kan mambobin jam’iyyar da kungiyoyin magoya baya a jihar.

Ya ce maganganun da ke fitowa daga bangarorin magoya bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma bangaren tsohon dan takarar gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da mataimakinsa Hon. Murtala Sule Garo, ba su da amfani ga zaman lafiya da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

 

Abbas ya bayyana cewa nadin shugaban NERC batu ne da ke ƙarkashin ikon Shugaban Ƙasa tare da amincewar Majalisar Dattawa, don haka ya kamata a bar su su yi aikinsu bisa doka da tsarin mulki.

 

Shugaban jam’iyyar ya kuma tunatar da mambobi cewa, duk da bambancin ra’ayoyi da ke cikin jam’iyya, APC ta dade tana tafiya bisa akidar haɗin kai, zaman lafiya da mutunta juna. Ya bukaci kowa da kowa ya zauna lafiya, ya guji kalaman da ka iya haddasa rikici, tare da mutunta doka.

A ƙarshe, Abbas ya bayyana tabbacin cewa Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Dattawa za su ɗauki matakin da ya dace, wanda zai fi amfani ga jama’a da

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button