Gwamnan Kano Ya Umurci Shugabannin Ƙananan Hukumomi Su Riƙa Gudanar da Taron Tsaro Akai-akai

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai, domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda aka bayyana cewa manufar tarukan ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma wajen gano da kuma magance barazanar tsaro tun kafin ta zama matsala.
Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su tsakanin al’umma, shugabanni da jami’an tsaro, yana mai cewa hakan ne kadai zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar wasu yankunan jihar.
Sanarwar ta ce wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotanni na hare-haren ’yan bindiga a wasu yankuna, musamman waɗanda ke iyaka da Jihar Katsina da sauran wuraren da ake fama da matsalolin tsaro.
Gwamnan ya yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su nuna jagoranci na gari, su kasance kusa da jama’a, tare da ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Kano.




