Siyasa

Jihar Kaduna: Jam’iyyar ADC Tayi wani zazzafan Gargadi

Shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihar Kaduna sun yi gargadi kan abin da suka kira yunkurin wasu ’yan siyasa na shiga cikin jam’iyyar da nufin kwace tsarinta, suna mai jaddada cewa jam’iyyar a jihar ta ginu ne kan gaskiya, jajircewa da aiki tuƙuru.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, Shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Ahmed Tijjani Mustapha, ya bayyana cewa mutanen da ke ikirarin suna cikin ADC a jihar ba su da wani hujja da ke tabbatar da cancantarsu daga matakin unguwa, ƙaramar hukuma har zuwa jiha.

Shugabannin ADC sun bayyana goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata David Mark, suna yabawa da irin jagorancinsa wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da tsari.

Sun kuma bayyana cewa korar wasu manyan jami’an jam’iyyar da aka ruwaito an yi, ba ta da inganci, suna kiran ta a matsayin yunkuri na wasu da ba su da rajista a jam’iyyar domin kwace iko.

Haka kuma, sun ƙi amincewa da cire shugabannin ƙananan hukumomi da suka fito daga zaɓen jam’iyyar na shekarar 2022, suna bayyana hakan a matsayin take hakkin jam’iyyar da cin karo da kundinta.

Shugabannin sun kuma bayyana cewa ba za su shiga rikicin siyasa tsakanin Nasir El-Rufa’i da Gwamna Uba Sani ba, saboda burinsu shi ne gina jam’iyya mai ƙarfi, ba maida hankali kan batutuwan waje ba.

Sun kuma shawarci mambobi da magoya bayan jam’iyyar su kasance masu faɗa a ji da kare jam’iyyar, tare da kiran abokan haɗin gwiwa su shiga jam’iyyar ta hanyoyin da kundin jam’iyya ya tanada, domin zaman haɗin gwiwa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button