Tsohon Kwamishinan Ilimi na Kano, Sanusi Kiru, ya soki yadda aka gudanar da aikin mayar da GGSS Maikwatashi zuwa Kaura Goje

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Sanusi S. Kiru, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka gudanar da aikin mayar da makarantar Government Girls’ Secondary School (GGSS) Maikwatashi zuwa Kaura Goje, yana mai cewa an yi manyan kura-kurai a cikin tsarin aikin.
A cikin wata wasika da ya aikawa Gwamnan Jihar Kano, Kiru ya yaba da kokarin gwamnati wajen inganta ilimi, amma ya bayyana cewa yadda aka aiwatar da wannan aikin bai dace ba.
Ya tunatar da cewa, a lokacin da yake kwamishina, an taba yin irin wannan sauyi a Jido Primary School, inda aka gina sabuwar makaranta gaba ɗaya tare da kayan aiki da kujeru kafin a mayar da ɗalibai. Wannan tsari, a cewarsa, ya taimaka wajen kauce wa tsaiko da wahala ga dalibai da malamai.
“Abin takaici, ba a bi irin wannan tsari ba a kan makarantar Maikwatashi. An rusa tsohuwar makaranta kafin a kammala sabuwar, abin da ya janyo wa ɗalibai da malamai wahala da rudani,” in ji shi.
Kiru ya ce masu kula da aikin sun nuna rashin kwarewa da sanin makaman aiki wajen tafiyar da irin wannan muhimmin tsari.
Haka kuma, tsohon kwamishinan ya nuna rashin jin daɗinsa kan hujjojin da aka bayar wajen rushe makarantar, musamman yadda aka nuna al’ummar Sabon Gari a matsayin masu laifi ko ‘yan daba, yana mai cewa wannan magana bata dace ba, duba da irin gudunmawar da al’ummar ke bayarwa ga ci gaban jihar da kuma rawar da suka taka wajen nasarar gwamnatin yanzu a zaben 2023.
Kiru ya kuma nuna damuwarsa kan rahoton da ke cewa filin tsohuwar makarantar ana sayar da shi ne kan naira miliyan ɗari (₦100,000,000) kowanne fuloti, yana mai cewa da ya fi dacewa gwamnati ta mayar da wurin zuwa filin wasanni, dakin taro ko wani abu da al’umma za su amfana da shi.
Haka kuma, ya soki maganganun da mai baiwa Gwamnan Kano shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yi a cikin wani faifan bidiyo, yana mai cewa bai kamata wanda ba shi da ruwa da tsaki a harkar ilimi ya rika magana a kan irin wannan batu ba.
Sai dai Kiru ya yaba da kwamishinan ilimi na yanzu, saboda yadda ya guji tsoma ma’aikatarsa cikin rikicin, yana mai cewa har yanzu akwai damar gyara kura-kuran da aka tafka.
A ƙarshe, tsohon kwamishinan ya bukaci gwamnatin Kano ta dauki darasi daga wannan lamari, domin ta inganta tsarin kula da harkokin ilimi a jihar cikin gaskiya, tsari, da tuntubar masu ruwa da tsaki.




