Kotu Tayi fatali da bukatar Bayar Da Beli Ga Tukur Mamu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da beli ga Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald, wanda ake tuhuma da tallafawa ayyukan ta’addanci.
Mai shari’a Mohammed Umar, wanda ya jagoranci zaman kotun a ranar Laraba, ya bayyana cewa babu hujjar bayar da beli, duk da roƙon da lauyoyin Mamu suka yi bisa dalilin cewa lafiyarsa tana bukatar kulawa ta musamman.
Sai dai kotun ta umurci Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da ke tsare da shi da ta kai Mamu asibiti mai inganci domin a duba lafiyarsa yadda ya kamata, tare da bashi damar zaɓar asibitin da yake so da kuma ganawa da iyalansa.
Mai shari’a Umar ya jaddada cewa masu gabatar da ƙara (prosecution) sun nuna jajircewa wajen gudanar da shari’ar, don haka babu dalilin bayar da beli bisa hujjar cewa an jinkirta shari’a.
Wannan dai shi ne karo na uku da kotu ke ƙin amincewa da belin Mamu tun bayan gurfanar da shi a ranar 21 ga Maris, 2023, bisa zargin aikata laifuka 10 da suka shafi tallafawa ta’addanci da makamantansu.
An kama Tukur Mamu ne a ranar 7 ga Satumba, 2022, a filin jirgin sama na Cairo a ƙasar Masar, inda daga baya aka dawo da shi Najeriya bisa zargin taimakawa ’yan ta’adda.
Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da shiga tsakani wajen tattaunawa tsakanin iyalan waɗanda aka sace a harin jirgin ƙasa na Abuja–Kaduna da ’yan Boko Haram, domin amfana da hakan ta fuskar kudi.




