An Kammala Zagaye Na Hudu Na Rigakafin Cutar Malaria A Jihar Kano

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta kammala zagaye na hudu (Cycle 4) na shirin Rigakafin Cutar Cizon Sauro (Seasonal Malaria Chemoprevention – SMC) a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Wannan zagaye ya gudana daga ranar Lahadi 19 zuwa Laraba 22 ga Oktoba, 2025, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCDA) da sauran abokan hulɗa a fannin lafiya.
Shirin SMC yana nufin kare yara masu shekaru daga watanni 3 zuwa 11 daga kamuwa da cutar Malaria ta hanyar rarraba magungunan kariya gida-gida da kuma wayar da kan jama’a kan tsaftar muhalli.
Ma’aikatar Lafiya ta bayyana cewa kammala wannan zagaye ya zo ne daidai da karshen damuna, lokacin da ake fara shiga lokacin sanyi da yawan sauro ke raguwa. Duk da haka, ma’aikatar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da tsabtace muhalli don kaucewa yaduwar cutar.
Rahotanni daga sassan lura da lafiyar jama’a sun nuna cewa, a bana (2025) an samu raguwar yawan masu kamuwa da Malaria a jihar, wanda hakan ke nuna nasarar hadin kai tsakanin gwamnati, ma’aikatan lafiya da abokan hulɗa.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya gode wa dukkan ma’aikatan lafiya da al’umma bisa goyon baya da jajircewa, tare da tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen lafiya masu inganci domin kare rayukan jama’a a fadin jihar.




