NUPENG Ta Dakatar da Shirinta na Yajin Aiki Bayan Cimma Matsaya da Dangote Refinery

Abuja, 10 Satumba 2025 – Ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya (NUPENG) ta dakatar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa, bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Refinery kan ’yancin ma’aikata na kafa ƙungiya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da NUPENG ta fitar a shafinta na X a daren Talata.
Cimma matsayar ta biyo bayan wata ganawa ta musamman da Hukumar DSS ta kira, wacce ta samu halartar Ministan Kuɗi, Wale Edun, tare da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC.
A cikin yarjejeniyar da aka sanya hannu, an amince cewa dukkan ma’aikatan kamfanin da ke son shiga ƙungiya za su samu damar yin hakan ba tare da wata tangarda ba, tare da fara tsarin nan da nan da kuma kammala shi cikin makonni biyu.
Yarjejeniyar ta kuma tabbatar da cewa ba za a zalunci wani ma’aikacin Dangote saboda batun yajin aikin ba.
Da wannan matsaya, NUPENG ta shelanta dakatar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa, yayin da aka amince cewa ɓangarorin biyu za su koma wajen Ministan Ƙwadago bayan mako guda domin bayar da rahoto kan yadda ake tafiyar da aiwatar da yarjejeniyar.




