NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa a Kano

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen Jihar Kano ta sanar da koriwar ɗan majalisar wakilai na mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyya da kuma kin biyan kuɗin da doka ta wajabta.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ne ya bayyana haka ranar Asabar a ganawarsa da manema labarai.
Dungurawa ya ce an kafa kwamitin sulhu domin tattaunawa da Kofa bayan ya bayyana ra’ayinsa a kafar Channels Television, amma maimakon ya yi amfani da wannan dama, sai ya ci gaba da sukar jam’iyya da shugabanninta.
> “Maimakon ya dawo domin tattaunawa, sai ya cigaba da yi mana adawa, har ma yana nuna biyayya ga wasu wajen waje da jam’iyya. Saboda haka muka yanke hukuncin korarsa, domin ba shi da wani ƙarin ƙima da zai kawo wa jam’iyya,” in ji Dungurawa.
Shugaban ya kara da cewa, ban da wannan, Kofa ya gaza biyan kuɗin da dokar jam’iyya ta tanada, abin da ka iya jawo daukarsa zuwa kotu domin karɓar kuɗin.
Ya kuma ce nasarar Kofa a zabe ba ta samo asali daga ƙarfin siyasar sa ba, illa kawai goyon bayan jam’iyya da kuma tasirin tafiyar Kwankwasiyya a ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso.
Dangane da jita-jitar yiwuwar Kofa ya koma jam’iyyar APC, Dungurawa ya ce hakan ba zai taba kawo illa ga NNPP ba, domin siyasa hadin kai ce, sannan tafiyar Kwankwasiyya na nan daram tana tare da Kwankwaso.




