Wadanda suka sami nasara a zaben cike gurbi da ‘akayi za su karbi takardun shaidarsu a ranar Alhamis-INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce za ta ba da takardun shaidar nasara ga waɗanda suka yi nasara a zaɓen cike gurbi na Agusta 16 a ranar Alhamis.
Mista Sam Olumeku, Kwamishinan Kasa na INEC kuma Shugaban, Kwamitin Bayani da Ilimin Masu Zabe, ya bayyana wannan a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.
Ya ce wannan shawarar ta yi daidai da tanadin Sashe na 72(1) na Dokar Zaɓe ta 2022.
Olumekun ya ce gabatar da takardun shaidar zababbun Sanatoci da zababbun ‘yan Majalisar Wakilai za a yi shi a hedkwatar INEC da ke Abuja da karfe 3:00 na rana.
Sanatoci da aka zaba da za su karɓi takardun shaidar zaɓe sun fito ne daga Yankin Sanatan Anambra ta Kudu da Yankin Sanatan Edo ta Tsakiya, da kuma mambobi biyar na Majalisar Wakilai da aka zaba, daga Mazabar Tarayya ta Ovie ta Arewa maso Gabas da Ovie ta Kudu maso Yamma a Edo, da Mazabar Tarayya ta Babura/Garki a Jigawa.
Sauran su ne Mazabar Tarayya ta Chikun/Kajuru a Jihar Kaduna, Mazabar Tarayya ta Ikenne/Shagamu/Remo ta Arewa a Jihar Ogun da Mazabar Tarayya ta Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo.
Mazabun sune Mazabar Jihar Ganye ta Adamawa, Mazabar Jihar Onitsha Arewa 1 ta Anambra, Mazabar Basawa da Zariya/Kewaye na Jihar Kaduna da Mazabar Bagwai/Shanono da Ghari/Tsanyawa na Jihar Kano.
Sauran su ne; Mazabar Jiha ta Okura a Kogi, Mazabar Jiha ta Munya a Neja da Mazabar Jiha ta Karim Lamido 1 a Taraba,” in ji shi.
Olumekun ya kuma bayyana cewa INEC ta tsayar da ranar 21 ga Agusta domin kammala zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe guda biyar na Mazabar Kaura Namoda ta Kudu a Jihar Zamfara.




