Labarai

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 bisa zargin aikata badala

Hukumar Hisba Ta Bayyana Cewa Ta Kama Wasu Matasa Maza Da Mata a Garin Dawakin Kudu Da Kuma Gadar Tamburawa

 

Mataimakin Kwamandan Hukumar Ta Hisba Na jihar Kano Mujahid Aminudden ne Ya Bayyana Hakan a Wata Sanarwa Da Ya aikewa da ya rabawa manaima labarai

 

Mun samu Korafe Korafe a Wadannan gurare kuma cikin ikon Allah mun Kai Samame wajen Kamar Yadda Al’umma Suka Bukata

 

Yace Samamen na haɗin gwiwa ne Tsakanin Jami’an Hukumar Da Hukumar NDLEA Kuma Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu acewarsa

 

Domin kuwa Sun Kama Maza 27 Sai Mata 35 wanda adadinsu ya zama 62 Kuma Hukumar zata ɗauki Matakin da Ya dace na Doka domin ya zama izina ga wasu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button