Labarai

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da a yanzu suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma

Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor.

 

Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan dabi’u ba.

 

Waiya ya bayyana cewa wasu daga cikin tubabbun mutanen da aka yi wa rajista a baya a cikin shirin sun riga sun rasu, inda gwamnati za ta sake gudanar da sabon aikin tantancewa domin sabunta bayanai.

Ya jaddada cewa wannan shiri ba na siyasa ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce kawar da matsalar ‘yan daba da sauran munanan halaye a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button