Labarai

Oluremi Tinubu Ta Kaddamar da Na’urori Don Yaƙi da Cutar Tarin Fuka a Najeriya

Mai dakin Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da sabbin na’urori na zamani don gano da kuma dakile cutar tarin fuka (TB) a fadin Najeriya, tare da bayyana aniyar ganin an kawar da cutar kafin shekarar 2030.

An gudanar da bikin kaddamarwar a Bwari, Abuja, karkashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI), wanda Sanata Tinubu ke jagoranta. Na’urorin an samar da su ne da kudin da suka kai Naira biliyan ɗaya, wanda aka yi alƙawarin bayarwa tun a ranar taron duniya kan TB da aka yi a Sauka, birnin tarayya.

Sanata Tinubu, ta bakin matar Gwamnan Jihar Kwara, Amb. Olufolake Abdulrazaq, ta ce na’urorin za su taimaka wajen gano cutar cikin hanzari, musamman a yankunan da babu wadatattun kayan gwaji. Ta jaddada cewa TB na da magani, amma rashin gano cutar da wuri na janyo mutuwar mutane da dama a ƙasar.

“Ya kamata mu ƙara saka jari a cikin gida – a samar da kuɗi da kuma ƙwararrun ma’aikata domin samun nasara a wannan yaƙi,” in ji ta.

A nasa jawabin, Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yaba da ƙoƙarin Sanata Tinubu, yana mai cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da haɗa shirye-shiryen yaƙi da TB cikin tsarin lafiyar matakin farko, da ƙarfafa ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya a matakai daban-daban.

Wannan mataki na daga cikin manyan sauye-sauyen da ake sa ran zai rage yaduwar cutar TB a Najeriya, tare da bai wa miliyoyin ‘yan ƙasa damar samun ganowa da magani cikin sauƙi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button