Shugaban Sojin kasan Nijeriya ya bukaci sabbin sojoji da su shirya don yaƙi da ta’addanci

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bukaci sabbin sojoji da suka kammala horo a makarantar horon aikin soja “Depot Nigerian Army” da ke Zariya, Jihar Kaduna, da su kasance a shirye domin yakar ta’addanci da ’yan tawayen da ke addabar ƙasar.
Yayin bikin yaye sabbin sojoji 6,195 na shigar dakarun zama na 88, Oluyede ya ja hankalin su da su kasance jarumai, kwararru, kuma masu juriya a fagen aiki. Ya ce rayuwar soja tana buƙatar sadaukarwa da kishin ƙasa, yana mai tunatar da su cewa sojoji ne masu kare martabar Najeriya.
Ya kuma jaddada muhimmancin kiyaye dabi’un rundunar soji irin su ladabi, biyayya, gaskiya, sadaukarwa, jaruntaka da mutunta jama’a. Ya bukace su da su yi aiki da ƙwazo da amana a duk inda aka tura su.




