Labarai

Nazo Kano ne domin na zama sabon Sarkin danben Nijeriya – Dogon kyallu 

Dan wasan Damben Nijeriya Dogon kyallu ya ce yazo jihar Kano ne domin zama sabon Sarkin Damben Nijeriya.

Kyallu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a filin dambe a jihar,inda ya ce yanzu babban burinshi shine sake zama sabon Sarki.

A ranar Lahadin data gabatane dai Sarki Ali kanin ballo da yafito daga bangaran Arewata ya sauka daga Sarautar danben Nijeriya bayan kammala wa’ adinsa kamar yadda dokar damben take.

Danben neman Sarautar dai ana fafatata ne a tsakanin bangarori uku da suka hada gurumada Arewata da kudawa.

Daga cikin wadanda suka nuna sha’awar shiga fafatawar domin neman Sarautar akwai Dogo Maitakwasara, Ali kanin Bello garkuwar Cindo,Dogon mai takwasara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button