Labarai

Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi gargadi ga ‘yan bindiga da ke yankin Zamfara da Katsina

Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi gargadi ga ‘yan bindigar da ke addabar jihohin Zamfara, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma da su fice daga maboyarsu.

Rundunar sojin ta kuma sha alwashin kara murkushe ‘yan ta’adda da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jihar Borno da sauran wurare a Arewa maso Gabashin Nijeriya, da kuma sauran masu aikata laifuka a wasu sassan kasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukuncin da rundunar sojin saman ta yi ya zo ne kasa da mako guda da aka yi ruwan hare-hare ga ‘yan ta’addan da ke zama a wasu kauyukan jihar Zamfara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button