Labarai

Hukumomi a Burikina Faso sun kamo masu ikirarin jihadi a yankin Sahel

A kwanan nan yawaitar ayyukan masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso sun kai wani matsayin da a baya ba yi zaton zai kai haka ba.

Ƙungiyar Al-Qaeda-mai alaƙa da Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta yi iƙirarin ƙaddamar da hare-hare fiye da 240 a tsakanin watannin Janairu da Mayun 2025.

Wannan ya riɓanya waɗanda suka ƙaddamar a shekarar 2024 da ta gabata.

Hare-haren ƙungiyar ta JNIM na nuna irin girman da ta ke da shi a yanzu, da kuma irin yadda ta ke ƙara ƙarfi, yayin da kuma aka lura da irin bidiyoyin da suke fitarwa na nuna ci gaban da suke samu ta amfani da fasahar zamani wajen isar da manufofinsu ga jama’a.

A daida lokacin da ƙasar ta Burkina Faso ke fama da munanan farmakin ƙungiyar ta JNIM, sai ga shi kuma cibiyar masu iƙirarin jihadin na ci gaba da nausawa zuwa kudancin ƙasar. Maƙwabciyar ƙasara wato Benin ita ma tuni ta fuskancin jerin hare-hare har 100 tun daga farkon wannan shekara. A bara JNIM ta kai hare-hare 23 a ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button